1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Yemen sun bayar da wa'adin kwanaki 10 na girka sabuwar gwamnati

Pinado Abdu WabaOctober 31, 2014

Tun bayan da aka tilastawa Ali Abdallah Saleh barin mulki a shekara ta 2011 Yemen ke fiskantar kalubalen mulki daga kungiyoyin 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/1DfLE
Jemen Rebellenführer Abdul-Malik al-Houthi 2013 KEINE BESSERE AUFLÖSUNG VERFÜGBAR
Shugaban 'yan tawaye Abdul-Malik al HuthiHoto: picture-alliance/dpa/Yahya Arhab

Daya daga cikin shugabanin yan tawaye mai karfin fada a ji a Yemen, ya gargadi shugaba Abdurabuh Mansur Hadi da ya girka sabuwar gwamnati tsakanin kawanaki 10 ko kuma su nada ta su ta aiwatar da irin aiyyukan da suke bukata.

Wasu 'yan tawayen da aka fi sani da Huthi, sun yi amfani da damarda suka samu a sanadiyyar rashin daidaiton da kasar ta soma fiskanta bayan faduwar gwamnatin Ali Abdallah Saleh a shekara ta 2011, suka kama babban birnin kasar na Sana'a ranar21 ga watan Satumba.

Wannan gargadin da aka yi wa Hadi na zuwa ne bayan da shugabanin 'yan tawayen suka gudanar da wani taron da ya sami halartar mafi yawan kungiyoyin 'yan tawayen kasar, da ma wadanda suka goyi bayan tilastawa Ali Abdallah Saleh ya ajiye mukaminsa.

'Yan kungiyar ta Huthi dai sun yi watsi da kiran da shugaba Hadi ya yi ranar lahadin da ta gabata, na cewa su kwance dammara su kuma janye mayakansu daga yankunan da suka kame, a ciki har da Sana'a babban birnin kasar ta Yemen, inda ya zarge su da kuntata wa jama'a a maimakon taimakon da suka ce suna yi