'Yan uwa na gurguzu: Jamus ta Gabas da Afirka
Angola da Habasha da Mozambik da kuma Tanzaniya: Kasar Jamus ta Gabas ta tafiyar da hulda ta kut da kut da kasashen Afirka 'yan tsarin gurguzu har zuwa karshenta sakamakon sake hadewarta da Jamus ta Yamma a 1990.
Karin ilimi a daura da yakin basasa
Har zuwa karshenta bayan sake hadewar Jamus a ranar 3 ga watan Oktoban 1990, Jamus ta Gabas ta horas da kwararrun ma'aikata daga kasashen Afirka 'yan gurguzu. A 1983 wannan dan Angola ya shiga tsarin neman ilimi na rabin shekara a cibiyar samun ilimin kare lafiyar ma'aikata a Dresden. A lokacin ana fama da yakin basasa a Angola. Jamus ta Gabas ta mara wa gwamnatin Markisanci ta MPLA.
Horas da 'yan jaridun Afirka
Baya ga fannin ilimin fasahohi, Jamus ta Gabas ta kuma horas da 'yan jarida daga Afirka. Daruruwan editoci daga ilahirin kasashen Afirka sun shiga darussan karin ilimi na makarantar kungiyar 'yan jaridu ta Jamus ta Gabas da ke a Berlin-Friedrichshagen. A wannan hoton dai matasa ne 'yan jarida daga Angola da Guinea-Bissau da Cape Verde hade da São Tomé da Príncipe a watan Disamban 1976.
Makaranta ta Abokantaka
Shugaban kasar Mozambik na farko, Samora Machel da Margot Honecker, ministar ilimin al'umma ta Jamus ta Gabas sun sadu da daraktocin Makarantar Abokantaka ta Straßfurter a 1983. A 1979 kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar cewa yaran Mozambik 899 za a aike da su makarantun kasar Jamus ta Gabas tsawon shekaru hudu.
Makarantar gaba da firamare ta "Dr. Agostinho Neto"
A lokacin ziyarar shugaban Angola, José Eduardo dos Santos, an ba wa makarantar gaba da firamare ta 26 a Berlin-Pankow sunan magabacinsa wato "Dr. Agostinho Neto", a watan Oktoban 1981. Membobin kungiyoyin matasan Jamus ta Gabas sun tarbi shugaban na Angola da kwalaye dauke da rubutuce-rubuce kamar: "Muna bayan Tarayyar Sobiet don zaman lafiya cikin tsarin gurguzu".
Ziyarar aiki a gaban katangar Berlin
A 1981 Shugaban Angola Eduard dos Santos ya kai ziyara harabar katangar Berlin da ke a kofar Brandenburg. A 1961 Jamus ta Gabas ta garkame katangar a bangaren Yammacin Berlin mai 'yancin walwala, don hana 'yan kasarta tserewa zuwa Yammaci. A hukumance ana kiran katangar "Ganuwar yaki da mulkin danniya". Mutane kimanin 200 sun mutu a kokarin tserewa.
Babban taron jam'iyyar SED tare da baki daga Afirka
A gun tarukanta, jam'iyyar gurguzu ta SED a Jamus ta Gabas tana jin dadin gabatar da kanta tare da baki na kasa da kasa. A rana ta 10 a taronta a 1981, Ambrósio Lukoki na kungiyar MPLA a Angola da Berhanu Bayeh wanda daga baya ya zama ministan harkokin wajen Habasha karkashin mulkin Markisanci sun halarci taron.
Ziyarar shugabannin jam'iyyar SED a Afirka
A daya bangaren ma kai wa juna ziyara ba sabon abu ne. Ga misali Konrad Naumann (dama a sahun baya), memba a kwamitin tsakiya na SED, ya halarci babban taron jam'iyyar neman 'yancin Afirka ta Guinea-Bissau wato PAIGC a watan Nuwamban 1977 a birnin Bissau. Taken taron shi ne "Mulkin Kai, Hadin kan kasa, Ci gaba".
Hutun karshen mako da baki daga Afirka
Yara baki da suka shiga hutun lokacin bazara a 1982, sun yi hutun karshen mako tare da iyalai na Jamus ta Gabas don nuna musu rayuwar yau da kullum ta kasar. An dauke su da jirgin kasa na musamman zuwa garin Schwedt mai masana'antar harhada magunguna da ke kan iyaka da kasar Poland. Sandra Maria Bernardo daga Angola ta samu kulawa daga Ingeborg Scholz da 'yarta Petra.
Taraktoci zuwa ga 'yan uwa na gurguzu
A wani matakin nuna zumunci, a shekarar 1979 an aike da taraktocin aikin gona masu yawa daga kamfanin kera taraktoci na Schönebeck zuwa ga tsohuwar gwamnatin Markisanci ta kasar Habasha. Taraktocin samfurin "ZT 300-C" da ake wa kallon masu inganci a kasar Jamus ta Gabas an sayar wa da kasashe 26 ciki har da Angola da Mozambik.
Injunan saka na Jamus ta Gabas a Habasha
Wadannan injuna a masana'antar tufafi ta birnin Kombolcha da ke lardin Amhara na kasar Habasha, suna samar da yadin shimfidan gado da tawul daga ulu. An dauki wannan hoto a watan Nuwamban 2005. A 1984 aka kafa masakar tare da tallafin Jamus ta Gabas da Cekoslovakiya. Kusan dukkan injunan sun fito ne daga Jamus ta Gabas.
Tsarin gine-ginen Jamus ta Gabas a Zanzibar
Har yau ana ganin irin wannan tsarin gini a Zanzibar, wanda a 1964 Jamus ta Gabas ta kafa kuma ta talafa wa kasar gurguzu ta Tanzaniya karkashin Shugaban kasa Julius Nyerere. Da jiragen ruwa aka yi jigilar kayan aikin ginin daga Jamus. A Zanzibar kuma aka harhada su zuwa gidaje. "Michenzani" ake kiran sabon tsarin gine-ginen da suka ci fili mai tsawon kilomita fiye da 1,5.
Begen Jamus ta Gabas a Maputo
Kimanin 'yan Mozambik dubu 15 ne suka yi aiki karkashin wani kwataragin aiki a Jamus ta Gabas har zuwa karshen shekaru gommai an 1980. Mafi yawansu sun koma gida bayan sake hadewar Jamus a ranar 3 ga watan Oktoban 1990. A can ana yi musu lakabi da "Jamusawa". Sukan yi zanga-zanga a babban birnin Maputo saboda rashin biyansu albashi daga bangaren Mozambik.