'Yan wasan tsallen Yuganda na kan alkiblar samun nasara
August 12, 2015Kadawar igiyar ruwa ba ta ba wa Rashid Etiau tsoro a duk lokacin da ya zo bakin tafkin Viktoriya don shafe tsawon lokaci ya na guje-guje. Hasali ma dai a bakin wannan ruwa ne akasarin 'yan tseren Yuganda suke samun horo kafin su wakilci kasarsu a gasannin kasa da kasa. Alal hakika ma dai Rashid na daga cikin 'yan wasan da aka fi ji da su a cibiyar horas da guje-guje da tsalle-tsalle ta Entebbe. Shi dai wannan matashin mai shekaru 19 da haihuwa, yana iya kokarinsa don ganin cewar ya shirya tsaf kafin gasannin da ke tafe.
"Ina aiki tukuru, saboda haka ne nake ganin cewar zan iya gudun ya na kanin wani na mita 800. Wannan ne zai bani damar haskani a duniya. Idan dai na halarci tseren kuma na ci, zai taimaka min cika buri na."
Goma ta arziki ake yi wa dan tseren Rashid Etiau ciki kuwa har da yi masa tausan jiki idan ya kare guje-guje. Ba don komai ba sai don tabbatar da cewar ya samu nitsuwa da kuma kulawa da za ta sa kwalliya ta biya kudin sabulu.
Dauniya don daukaka sunan kasa
Moise Asonya wanda tsohon dan tseren ne, shi ne yake horas da Rashid a kullu yaumin. Ya na wannan dawainiya ne domin kasarsa Yuganda ta shiga cikin sahun kasashen da sunayensu ke haskawa a fagen motsa jiki.
"Muna fama da karancin lambobi a wannan kasa tamu, saboda haka ne nake da burin horas da matasa don su ciwo wa wannan kasa lambobi."
Domin tabbatar da cewar hakarsa ta cimma ruwa ne ya sa Moise Asonya kafa cibiyar Entebbe da ke horaswa a fannin guje-guje da tsalle-tsalle tun shekaru biyu da suka gabata. Shi kadansa ne ke samar da kudin da ake tafiyar da wannan cibiya.
Karancin wuraren horas da 'yan wasan tsere
'Yan tseren Yuganda dai ba su saba lashe tsere na gajeren zango ba, saboda duk 'yan tserenta masu cin dogon zango ne, wadanda kuma galibinsu mazauna karkara ne. Sai dai kuma ba su da takamaimen filin da suke samun horo, lamarin da ke bakanta ran Moses Asonya.
"Muna da zaratan 'yan wasa a nan Yuganda. Idan da gwamnati za ta tallafa wa hukumomin da ke kula da wasanni, ka ga da za mu ci gaba da samun dimbin 'yan tsere a kasar nan."
Rashid Etiau na daga cikin 'yan tseren da ake ganin cewar ya na da rabon ganin badi. Ya taso ne a garin Serere da ke da nisan daruruwan kilometa da Kampala babban birnin kasar. Iyayensa marasa galihu ne, saboda haka ba za su iya taimaka masa ba. Sai dai kuma Rashid ya ce gatar da ya samu daga Asonya za ta bashi damar cika burin da ya sa a gaba, na lashe tsere a wata muhimmiyar gasa a ketare.
"Idan dai abin da ya shafi horo ne, coci na taimakamin yadda ya kamata. Na san cewar zan kai labari. Kullum cemin yake yi Rashid kana da bajinta. Ci gaba da mayar da hankali a kan horo. Saboda haka ne nake mayar da himma ni da sauran 'yan tseren. Na san cewa watan watarana zan ba wa marada kunya."
Rashid da wasu 'yan tsere biyar da cibiyar horaswa ta Entebbe sun yi nasarar shiga cikin rukunin 'yan wasa da za su kare martabar Yuganda nan gaba.