Zafi ya yi kamari a Kano
April 9, 2019
A wannan lokaci da zafin ranar kan zarta degree 40 a ma'aunin zafi, babu abunda jama'a suka fi yi face yawaita shan ruwan sanyi da wanka da ruwan sanyin, a daidai lokacin da suke cigaba da gudanar da harkokinsu a takure.
Direbobi da ke tafiya mai dogon a yankin arewacin Najeriyar, sun koka da yanayin na zafi, sai dai sun ce idan suka tsaya ne lamarin yafi yawa, domin a yayin da suke tafiya iska na dan fifitasu.
Wasu 'yan kasuwa da ke tafiyar da harkokinsu na kasuwanci a kan ranar kuwa, sun koka da hali mawuyaci da suke ciki, inda wasu kan koma gida su dan watsa ruwan sanyi, kafin su sake komawa bakin harkokinsu na kasuwanci. A yayin da wasu da ba zasu iya komawa gida ba kan bi inuwa inuwa domin samun saukin lamarin.
Su ma dabbobi a ba a barsu a baya ba na jin radadin yanayin na zafi, saboda karancin abinci.