1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin kallon kwallon duniya a Najeriya

June 11, 2014

Jami'an tsaron jihar Plateau sun bayyana cewar za su karfafa tsaro a cibiyoyin kallon kwallo, don tabbatar da cewar ba a fuskanci hare-hare lokacin kofin duniya na Brazil ba.

https://p.dw.com/p/1CGmj
Hoto: NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images

Hukumomin sun dauki matakan na tsaro ne sakamakon hare haren da aka kai cibiyoyin kallon kwallon kafa a Jos, lamarin dake neman janyo tsoro a zukatan masu sha'awar wannan wasa. To sai dai kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Plateau Felicia Aslem, ta ce za su " samar da cikkaken tsaro a dukkanin cibiyoyin kallon kwallon kafa dake cikin jihar a lokacin gasar ta kofin duniya. Hakan ya zama wajibi don tabbatar da ganin mun kare daukaccin masu kallon kallon:"

Shugaban kungiyar masu gidajen kallon kwallon kafa a jihar Plateau Zakari Mohammed, ya shaida wa DW Hausa cewar sun yi zama a lokuta daban daban da jami'an tsaro gabanin gasar ta kofin duniya, don daukan matakan da sua wajaba. A kwanakin baya ne dai wasu mahara suka nufin wani gidan kallon kwallon kafa a nan Jos, sa'ilin da ake gassar karshe ta kofin zakarun Turai. Ko da shike basu cimma gidan kallon ba, amma kuma bam din ya tashi.

Interaktiver WM-Check 2014 Mannschaft Nigeria
Hoto: picture alliance/augenklick

To amma kuma ra'ayoyi sun banbanta tsakanin masu sha'awar zuwa kallon a gidajen da ake nuna wassannin. Ranar Alhamis ta wannan makon ne dai ake soma gasar ta kofin duniya a kasar Brazil.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa daga Jos
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe