Yanayin zamantakewar Iyalai a Togo
May 16, 2013Duk da cewa akwai ranaku na musammman da Majalisar Ɗinkin Duniya ke keɓewa domin tunawa da mata, har yanzu akwai matan da ke ci gaba da wahala a kasashen daban-daban na Nahiyar Afirka, wannan rahoton ya duba mana rayuwar wata mata mai gudanar da aikin dako a babbar kasuwar birnin Lome na kasar Togo
Mallama Essi Djade kenan yar kimanin shekaru 50 da haifuwa, ta ke bayyana irin matsalolin da ta ke cin karo da su a wajen gudanar da aikin na dako wacce ta ci gaba cewa, wasu mutane ba sa tausaya mana suna nuna hasalarsu a hili, suna furta muna miyagun kalamai na zagi, kai har birai su ke kiran mu wai ba zamu samu abin za mu ci ba.
Aikin dako aiki ne mai wahalar gaske a wajen maza ma ballantana mata kuma mallama Djade ta share aƙalla shekaru 15 ta na gudanar da wannnan aiki, to ko me ya tura ta ga shiga wannan aiki na doko?
"Talauci ne da fatara suka tilasta min shiga wannan aiki, kuma ina mai tabbatar maka da cewa ba daɗi sai wahala, ka diba ka gani a tsawan inin jiya dala 100 kawai na samu, ga shi kuma a yau zan sauka da dala 25r kawai, kai a gaskiya aiki ne mai tsananin wuya gashi kuma kayan da mu ke dauka su na da nauyin tsiya".
A samakon ƙuncin rayuwar da mallama Djade ta kasance a ciki, da kasancewar kuma mijinta ya jima da rasuwa haka ta ke faɗi tashin kula da 'ya 'yan ta marayu guda hudu.
"Wannan shi kawai ne aikin da zan iya yi domin ciyar da 'ya 'ya na in kuma samu abinda zan biya kuɗaɗan karatun su, idan kuma na ƙi yin wannan aiki ai sai shiga sata, ka ga saboda haka mu ke zuwa nan Lome muna gudanar da wannan aiki".
Babu wani taimako da ta ke samu haka ta ke ci gaba da tattara 'yan kuɗaɗan tana kula rayuwar iyalin ta, fatan ta shi ne kar ta kamu da rashin lafiya, inda kuma ta bada shaidar idan mai aikin dako ta kamu da rashin lafiya.
Essi Jade ta kara da cewa wani lokaci su na samun hatsarin ababan hawa musamman ma na 'yan Acaba, ba su kuma kulawa da su, wani sa'in su ken kama gaban su suna kuma zangin su.
Mata da dama da ke wannan sana'ar ta dako irin su Essi Djade na da yawan gaske kuma su na yin sana'ar ce a cikin irin wannan mawuyacin halin kuma akasarinsu mazauna karkara ne da ke zuwa cikin birane su na gudanar da irin wannan aiki.
Mawallafi: Yusuf Abdoulaye
Edita: Umaru Aliyu