Afghanistan: Murna da fargabar sulhu
March 23, 2020Yarjejeniyar da aka cimma a birnin Dohan kasar Katar ta sanya tsallen murna, sai dai ba haka yake a wajen matan kasar da rayuwarsu ta inganta matuka cikin shekaru 19 da suka gabata a kasar ta Afghanistan ba. Yara mata sun samu damar zuwa makaranta abin da aka haramta lokacin mulkin Taliban. A fannonin rayuwa da dama, mata na taka muhimmiyar rawa har ma da fita domin samun ayyukan yi, sabanin tsakanin shekarar 1996 zuwa shekara ta 2001 da Taliban ke rike da madafun ikon kasar, inda mata ka iya yin aiki ne kawai a gida ko kuma a boye.
Fargabar ci gaba da take hakkin mata
Hameda Safi tana tafiyar da shagon sayar da kayan sakawa a birnin Kabul fadar gwamnatin Afghanistan, a cewarta ba ta yarda da alkawarin da Taliban ta yi na cewa za ta mutunta yarjejeniyar ba, musamman ma kan batutuwan da suka shafi kare hakkokin matan kasar. Ita ma a nata bangaren Shukria Jalaljzay da ke rajin kare hakkin mata a kasar, ta nuna fargabara cewa galibin matan Afghanistan da suke da ilimi za su tsere daga kasar idan Taliban ta sake samun madafun iko.
A bayyane yake cewa har yanzu babu wanda ya iya fahimtar kalaman Taliban kan matsayinsu dangane da makomar matan Afghanistan a cikin al'umma. A wani yanayi na mayar da duniya baya, karkashin tsarin daular da suke kira da ta Islama, lokacin mulkin Taliban maza kadai ke da ta cewa.
Mata sun samu 'yancin yin ayyuka
Mai magana da yawun kungiyar Taliban Mohammad Suhail Shasheen ya shaidawa kafar talabijin ta Jamus ta ARD cewa tilas mata su bi tsarin dokokin addinin Islama nan gaba.
Matan dai a yanzu suna taka rawa a siyasar Afghanistan din suna kuma yin aiki a matsayin masana kimiya da 'yan jarida ko aiki na kashin kai. Suna fagen wasanni da wakoki da duk sauran abubuwan da aka haramta a baya karkashin mulkin kungiyar Taliban da ta ce sun saba da tsarin addinin Islama da kuma ake tunanin za su sake hanawa a gaba. 'Yancin matan na cikin abin da za a tattauna tsakanin mutanen Afghanistan, amma kungiyar Taliban na tunanin maza ne kadai ya kamata su mamaye komai.