'Yancin shigi da fici na janyo cece-kuce tsakanin kasashen kungiyar EU
November 4, 2014A Ingila, muhawara game da yiwuwar ficewar kasar daga kungiyar hadin kan Turai tana kara tsananta, musamman yadda ake danganta wannan muhawara da batun yancin shigi da ficin jama'a a kungiyar ta hadin kan Turai. Jaridar Guardian ranar Litinin a shafinta na Intanet ta gabatar da wani rahoto game da wani jawabi da aka ce shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi, game da yiwuwar ficewar Ingila daga kungiyar. Wannan rahoto, inji jaridar ya dauki hankali matuka a Ingila.
Jaridar Guardian ita kanta ranar Lahadi ta rawaito cewar Merkel ta ce a shirye ta ke ta amince da ficewar Ingila daga kungiyar ta hadin kan Turai, muddin Ingila din ta nuna alamun ba za ta ci gaba da amincewa da yancin shigi da fici tsakanin al'ummar kungiyar ba. Jaridar Guardian, kamar sauran jaridu da dama a kasar ta Ingila, ta ambaci wani rahoto ne na mujallar labarai ta Jamus wato Spiegel.
A rahoton mujallar na ranar Litinin, ta nunar da cewar gwamnatin Jamus tana sa ran zai zama tilas Ingila ta janye daga kungiyar hadin kan Turai, idan har ta nemi tauye yancin shigi da fici a wannan kungiya. Mujallar Spiegel ta ambaci wata majiya wadda ta saurari tattaunawa a taron kolin baya-bayan nan tsakanin Angela Merkel da Pirayim minista David Cameron na Ingila.
'Yancin shiga da fici tsakanin Turai na da mahimmanci
To sai dai jim kadan bayan haka, kakakin gwamnati a Berlin, yayi kokarin yin gyara ga abin da mujallar ta Spiegel ta ce ta ji, inda ya ce shugabar gwamnatin, a ganawarta da manema labarai lokacin taron kolin kungiyar hadin kan Turai ranar 24 ga watan Oktoba cewa tayi:
"Jamus ba za ta kyale wani ya nemi taba tsarin nan na yancin shigi da fici tsakanin kasashen kungiyar hadin kan Turai, wato EU ba. To amma hakan ba yana nufin wannan tsari ba ya tattare da matsaloli iri dabam dabam bane."
Cikin matsalolin da Merkel take magana kansu kuwa, har da yadda za a hana 'yan kasashen na kungiyar EU shiga wasu kasashenta domin karbar kudaden taimako da ba sa samu a kasashensu. Karar da Jamus ta kai gaban kotun kololuwa ta kasashen Turai yanzu haka tana jira a saurareta, inda ake sa ran kotun za ta yanke hukunci a watan Nuwamba.
David Cameron ya goyi bayan ficewa
A nashi bangaren, Pirayim ministan na Ingila, kamar yadda wani rahoto na jaridar Sunday Times ya nunar, ya ce matakin da kadai ya ke shirin dauka shi ne tilastawa yan kasashen Turai su fice daga Ingila, idan bayan watanni uku a kasar suka nuna alamun ba za su nemi yadda za su iya rike kai da kansu ba.
"Duk wani kokari da wani zai yi na gaban kansa domin yiwa shirin na yancin shigi da fici zagon kasa, a ganina, abu ne da ba zai dace da dokokin kungiyar hadin kan Turai ba. Mu a garemu, manufar nan ta daidaituwa tsakanin yan kasashen Turai abu ne mai muhimmanci kamar yadda yancin shigi da fici shima yake da muhimnci. Hakan kuwa ya shafi kayan ciniki da zuba jari da hidimomi da shigi da ficin jama'a."
Wannan fushi na Cameron ba ya samu ne saboda takaddamar shigi da ficin jama'a ba, amma sai saboda kudin da hukumar kungiyar hadin kan Turai tace Ingilan da sauran kasashen EU su biya a asusun wannan kungiya.