1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki: daurin rai da rai ga 'yan IS

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
August 6, 2018

Wata kotu a Iraki ta yankewa wata 'yar kasar Jamus mai shekaru 22 da kuma wani dan kasar Faransa mai shekaru 55 a duniya, hukuncin daurin rai da rai sakamakon samun su da laifin shiga kungiyar 'yan ta'addan IS.

https://p.dw.com/p/32gwH
Irak US Military Holds Thousands Of Detainees In Baghdad Prison
Hoto: Getty Images/J. Moore

Kungiyar ta IS dai ta addabi Irakin da Siriya tsawon lokaci, inda ma har ta yi ikirarin kafa daula, kafin a tilasta musu fita daga mafi akasarin yankunan da suka kama a kasashen biyu.

Yayin yanke hukuncin da mai shari'a Suhail Abdullah ya karanta a kotun hukunta masu aikata manyan laifuka da ke Bagadaza babban binin kasar, jami'an ofishin jakadancin kasashen Jamus da Faransa da kuma masu fassara sun halarci zaman kotun. Dama dai tuni aka yankewa 'yar kasar Jamus din hukuncin shekara guda a gidan kaso sakamakon samun ta da laifin shiga Irakin ba bisa ka'ida ba da kuma shiga kungiyar 'yan ta'adda.

Rahotanni sun nunar da cewa akwai mata masu tarin yawa daga kasashen yammacin duniya, da suka shiga kungiyar ta IS a kasashen na Iraki da Siriya.