1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yankin gabas ta tsakiya

January 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuU5

Majiyar gwamnati na nuni dacewa,Izraela na shirin tura kudi kimanin dala million 100 daga cikin asusun palasdinawa data rufe,zuwa ga hukumomin yankin nanda saoi 24.Wannan kudin dai na bangaren kimanin dala million 660 da Izraelan ta karba a matsayin kudaden haraji,amadadin hukumar palasdinawan,wanda kuma ta dakatar da basu,tun da kungiyar hamas ta fara mulkin wannan yanki a watan janairun 2006.wadannan kudaden dai zasu taimaka wajen rage matsalolin kudi da alummar palasdinawan ke fama dasu,wanda kuma aka cimma yarjejeniyarsa a ganawar shugaba mahmoud Abbas na yankin da Premiern Izraela Ehud Olmert a watan Disamban daya gabata.