Yankin Kataloniya ya ayyana yancin kai
October 27, 2017Majalisar dattijan Spain ta umarci gwamnatin Firaminista Mariano Rajoy ya karbi ragamar mulkin Kataloniya tare da gudanar da sha'anin mulkin yankin kai tsaye daga Madrid.
A yanzu dai Firaminista Rajoy zai gudanar da taron majalisar ministocinsa domin daukar matakin farko na gudanar da mulkin Kataloniya.
Sai dai kuma yan mintuna bayan matakin majalisar dattijan, yankin na Kataloniya ya sanar da ayyna 'yancin kai.
A zaman majalisar Kataloniya, yan majalisa 70 suka kada kuri'ar goyon bayan ballewa yayin da yan majalisa 10 suka kada kuri'ar rashin amincewa 2 kuma suka kasance yan baruwanmu.
Kawo yanzu dai babu wata kasa a duniya da ta goyi bayan ballewar yankin na Kataloniya.
A halin da ake ciki Firaministan Spain Mariano Rajoy ya bukaci jama'a su kwantar da hankula.