Yankin Kataloniya zai tsahirta ficewa
October 11, 2017Talla
Shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont, a ranar Talata ya bayyana dakatar da shirin ballewar yankin daga Spain sai dai ya bayyana bukata ta zaman tattaunawa a matsayin mataki da zai sanya yankin kama hanyar ficewa daga kasar Spain.
A cewar Puigdemont kuri'ar raba gardamar da aka kada daya ga watan nan na Oktoba ta bawa yankin dama na cin gashin kai sai dai za a dakatar da yin hakan har sai an sake tattaunawa da mahukuntan Madrid.
Yanzu dai hankali ya karkata kan gwamnatin tsakiya inda a wannan rana ta Laraba Firmanista Mariano Rajoy ya kira taron majalisar ministocinsa cikin gaggawa, bayan da a baya ya yi watsi da duk wata tattaunawa da masu rajin ballewar.