'Yar gudun hijirar Sudan ta zama mai gyaran mota a Libiya
Asawar Mustafa ta guje wa yaki a kasarta Sudan, bayan ta bar karatun harhada magunguna a shekarar karshe a Jami'a. A yanzu ita ce mace daya tilo mai gyaran mota a Libiya, ta samu sabon abin da take kauna.
Gareji ya shaidar da kyakkyawan fata
Mai shekaru 22 da haihuwa 'yar gudun hijirar Sudan, Asawar Mustafa na duba soson tace mai a bangaren mata zalla na wani gareji a Misrata na Libiya. A kasar ta Afrika, ana aikin gyaran mota a matsayin aiki na maza kawai. Wannan bai sare wa Asawar gwiwa ba, inda ta ci gaba da rayuwa bayan ta tsere daga kasarta da yaki ya daidaita.
Mutane na cewa "Zaman gida ya fi dacewa da ke"
Bangaren mata zalla na garejin nan ne Asawar ta baje basirarta, duk da cewa ta na tsoron lalata motar jama'a da suka kawo gyara. Mutane na gaya mata cewa kichin ne ya dace da ita, amma sai ta mayar da sukar zuwa kwarin gwiwa maimakon ya zame mata cikas.
Amfani da hada magunguna a fasahar kanikanci
Ko da yake da farko ta shiga harkar harhada magunguna ne, a yanzu ta samu kwanciyar hankali a kanikanci, inda ta gano alaka tsakanin kwarewar hada magunguna da hikimar gyaran mota. Ita ce kadai mace ma'aikaciya a garejin, ta kuma samu goyon bayan wanda ya dauke ta aiki Abdelsalam Shagib, wanda ke son fadada ma'aikatansa.
Mistrata na Libiya, dama ta fara kanikanci daga tushe
Mustafa wacce da take 'yar shekara 21, tare da 'yan uwanta mata su hudu da mahaifiyarta da kuma kaninta. sun guje wa yaki a Sudan, inda suka shafe kwanaki 10 a cikin hamada. Sun isa Kufra, inda 'yan gudun hijirar Sudan fiye da 40,000 suke zaune. Garin na tazarar 1,200 daga Misrata, inda a karshe ta samu aiki.
Mata direbobi sun ji dadin samun mace makanikiya
A yanzu ta Asawar Mustafa na jawo mata direbobi da dama wadanda ke samun sakewa da mace makanikiya. Mata da ke tuka mota a Libiya sun samun kwanciyar hankali a inda suke gani suna hulda da mace 'yar uwansu mata. Sabanin idan suna hulda da maza suke jin fargaba.
Rikicin Sudan ya tagayyara miliyoyin mutane
Iyalan Mustafa sun tsere daga Sudan a cikin watan Oktoba 2023. Yakin basasar kasar tsakanin sojojin gwamnati da sojin sa kai na RSF ya halaka dubban mutane yayin da sama da mutane miliyan 10 suka rasa muhallansu. Wasu mutanen miliyan biyu da dubu dari uku suna gudun hijira a kasashe kamar Libiya.
'Yancin mata na karuwa a Libiya
A 2022, an yi kiyasin cewa kashi 37% na mata na aikin karfi a Libiya. A karkashin mulkin Gaddafi, mata na fadi tashi don samun 'yanci na harkokin kudade. Mata kamar Mustafa wadanda suke jure wa dukkan yanayi suna samun nutsuwa da kuma karfafa wa sauran mata gwiwa, hatta a bangarori da ake gani ba su dace da mata ba.