1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF: Yara na fama da karancin abinci

Abdoulaye Mamane Amadou
June 23, 2022

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kananan yara miliyan takwas na fuskantar barazanar mutuwa sakamakon matsalar tamowa da wasu kasashen duniya ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/4D6NI
Hungersnot am Horn von Afrika
Hoto: Zerihun Sewunet/UNICEF/AP Photo/picture alliance

A cikin wani rahoton da ya fitar a wannan Alhamis, asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya ce a cikin kasashe 15 ne matsalar ta fi kamari inda kananan yaran ke cikin halin ni 'yasu saboda rashin wadataccen abinci, sai dai rahoton ya kuma bayyana hudu daga cikin kasashen da suka hada da Afghanistan da Ethiopia da Haïti da Yémen da a matsayin wadanda barazanar ta fi daukar hankali da muni a wannan shekara.

Wasu daga cikin dalilan da asussun ya ambata  da ke zama musabbabin barazanar su ne matsalar fari sakamakon karancin ruwan sama, da canjin yanayi da illolin da annobar corona ta haifar da kuma tashin-farashin kayan abinci da duniya ke fuskanta a yanzu sakamakon mamayar Ukraine take fusknata daga makwabciyarta Rasha.