1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara na mutuwa a cikin teku

Zainab Mohammed Abubakar
July 14, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin yara 289 ne aka san sun mutu a farkon rabin shekarar 2023, a yayin da suke kokarin tsallakawa tekun Bahar Rum zuwa Turai.

https://p.dw.com/p/4Tv4Q
Symbolbild | Ocean Viking rettet Migranten
Hoto: Valeria Ferraro/AA/picture alliance

Adadin ya ninka wanda aka samu a watanni shida na farkon shekarar 2022, in ji asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, tare da kira da a fadada hanyoyin mafi inganci da bin doka ta hanyar bude wa yaran damar neman kariya a Turai.

Shugabar sashin kula da masu kaura da wadanda suka rasa matsugunnansu ta hukumar UNICEF Verena Knaus, ta ce a zahiri alkaluman na iya zarta haka, saboda hadarin nutsewar jiragen ruwa sau da yawa a tsakiyar tekun Bahar Rum, ba tare da wani ya tsira da ransa ba, ko kuma ba a rubuta su ba.

A cewar UNICEF, a cikin watanni ukun farko na shekarar 2023 da muke, kusan yara 3,300 wato kashi 71 cikin 100 na dukkan yaran da suka isa Turai ta hanyar teku, na rubuce ne a matsayin wadanda ba su da mai rakiya ko kuma an raba su da iyayensu.