1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara za su shiga halin tasku a kusurwar Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar M. Ahiwa
December 23, 2022

Kananan yara a Somaliya da Habasha za su fi fuskantar matsaloli a 2023. Baya ga yakin Ukraine, rashin mulki na gari na taka rawa, a cewar Ludger Schadomsky na tashar DW.

https://p.dw.com/p/4LNo3
Hoto: Feisal Omar/REUTERS

Ludger Schadomsky ya fara sharhin nasa ne yana mai cewa: Masu sanya idanu kan al'amuran da ke faruwa a yankin kahon Afirka, ba su yi mamaki ba da suka ji wannan bayani daga kwamitin ayyukan ceto na kasa-da-kasa wato International Lobby Committee da Albert Einstein ya kafa a shekara ta 1933. A shekara ta 2023 ba kasashen Ukraine da Siriya ko Yemen da ke fama da yaki ne abin damuwa a duniya ba, sai dai kasashen Somaliya da Habasha. Ko ta yaya aka kai ga shiga wannan hali?

Tsawon shekaru biyu kasashen na fama da fari gami da yakin da ake fafatawa tsakanin rundunar sojojin da ba ta da wani karfi da kuma 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi na al-Shabaab da ke da alaka da kungiyar al-Kaida, ba abun mamaki ba ne idan aka kira Somaliya da rusasshiyar kasa da ke yankin Kahon Afirka da ta sha gaban duk wani mummunan labari. Yayin da mutane da dabbobi ke fama da yunwa, shugaban kasa da firaminista da sauran 'yan majalisun dokoki da aka zaba, sun tsunduma kansu a badakalar cin hanci da fifita makusantansu tare da yin watsi da halin da kasar ke ciki. 

Ukrainischer Weizen für Afrika | Weizenmehl auf dem Markt in Mogadishu
Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP/picture alliance

Kwatsam kuma sai Rasha ta kai farmaki Ukraine, kana Somaliya na samun kaso 90 cikin 100 na alkama daga kasashen na Rasha da Ukraine. Tallafin abinci da ke isa Somaliya a yanzu, bai fi karin maganar nan da ake cewa digon ruwa cikin teku ba. Yara kimanin dubu 500 na fuskantar barazanar yunwa sakamakon fari da yaki da kuma karancin tallafi fiye da kowacce kasa a duniya. Rikici na din-din-din da ake fama da shi a kasar mai albarkatun koguna na kamun kifi, na barazanar shiga makwabta idan aka kwatanta da yankin Somaliland mai kyakkyawan shugabanci da kuma ya kasance wani yanki da ke tuna wa kasashen Yamma cewa akwai Somaliya.

Ya kamata wadanda ke dora alhakin halin da ake ciki ga kasashen Yamma su sani, duk da badakalar da Somaliya ke ciki Amirka ke bayar da kaso 90 cikin 100 na tallafin da ake kai wa zuwa kasar da ke cikin rudani. Shugabannin kasashen da ke cikin wannan halin ne kadai za su iya fitar da su, sai dai abin takaici babu alamar hakan.

Ita kuwa fagen daga kasar Habasha, ta kwashe tsawon shekaru biyu cikin gwabza fada tsakani dakarun gwamnati da na mayakan yankin Tigray TPLF. Kafin tsagaita wuta a watan Nuwambar da ya gabata, yakin da ya kasance mafi muni da tsada a tarihin duniya a baya-bayan nan, ya shafi kimanin mutane dubu 600. Kudin kowanne jirgin yaki mara matuki na Turkiyya samfurin Bayraktar TB2 da gwamnati ta yi oda daga Ankara, ya kama tsakanin Euro miliyan biyu zuwa miliyan biyar. Gwamnatin ta bayyana cewa tana bukatar Euro miliyan uku da dubu 400 domin sake gina kasar, kudin ka iya haura haka, a daidai kuma lokacin da kasar ke fama da hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kaso 40 cikin 100.

Türkei | Das türkische UAV bewaffnete Drohne „Bayraktar TB2“
Hoto: Baykar/AA/picture alliance

Yayin da kasashen Somaliya da Habasha ke cikin halin rashin tabbas a shekara mai zuwa, a hannu guda babu wanda ya san halin da ake ciki a makwabciya Iritiriya ko kuma Koriya ta Arewan Afirka. Babu rahoto kan COVID-19 ko kuma yunwa, kasar da ke da muhimmanci ta gabar Tekun Bahar Maliya na zaman abu a duhu. Abin da kawai yake a bayyane, shi ne shugaban mulkin kama-karya na mutu ka raba, Isaias Afwerki da zai ci gaba da shugabanci a kasar da ka iya sake haifar da rudani a shekara ta 2023 cikin yankin.

Duk da yakin da ake fama da shi a Ukraine, bai kamata Jamus da kasashen Turai, su yi watsi da halin da ake ciki a yankin na Kahon Afirka ba. Yin hakan ka iya janyo kwararar 'yan gudun hijira da ke bi ta Tekun Bahar Rum zuwa Turai, abin kuma da ka iya haifar da matsalolin zamantakewa da ma rayuwa a kasashen na Turai.