1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al Sissi ya yi wa Bin Salman lale marhabun

Abdullahi Tanko Bala
November 27, 2018

A karon farko tun bayan tuhumar kisan dan jarida Jamal Khashoggi, yarima mai jiran gadon saudiyya Mohammed bin Salman na rangadi a wasu kasashen Larabawa.

https://p.dw.com/p/38zdc
Kairo Prinz Mohammed Bin Salman bei   Abdel Fattah al-Sisi
Hoto: Reuters/Egyptian Presidency

Shugaban Masar Abdel-Fatah al Sissi  ya yi wa yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman kyakkyawar tarba a birnin Alkahira a ziyararsa ta farko ta rangadin wasu kasashen larabawa wanda ke zama ziyara ta farko zuwa kasashen waje tun bayan tuhumar kisan gillar da aka yiwa dan jaridar nan Jamal Khashoggi.

Shugaban Masar Abdel fattaha al Sissi da ke dasawa da kasar Saudiya wanda kuma kasarsa ke samun tallafin kudi daga Saudiyya ya tarbi yarima Mohammed bin Salman a filin jiragen sama.

Shugaba al Sissi ya marawa Saudiyya baya kan batun kisan Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya dake Istanbul inda yace kafofin yada labarai sun taka rawa wajen yada labarai mara dadi a kan kisan yana mai gargadi kan kokarin wargaza Saudiyya.

Kafin ya kai ziyara Masar sai da yarima Bin Salman ya ziyarci kasar hadaddiyar daular Larabawa da kuma Baharain. Yana kuma shirin kai ziyara Argentina domin halartar taron kungiyar G20 ta kasashe masu cigaban masana'antu ta duniya.

Can kuwa  a kasar Tunisiya dubban 'yan kungiyoyin farar hula da masu rajin kare hakkin dan Adam da 'yan jarida sun yi dandazo domin adawa da ziyarar yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyyar Mohammed bin Salman.