Yarima William na Ingila zai gana da Donald Trump a Paris
December 7, 2024Yarima William na Burtaniya zai gana da zababben shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump a birnin Paris a wannan Asabar, yayin da shugabannin kasashen duniya suka amsa gayyatar shugaban Faransa Emmanuel Macron, don halartar bikin sake bude mujami'ar Notre-Dame da aka yi kwaskwarima bayan gobara ta kone ta a shekarar 2019.
Karin bayani:Notre Dame: Duniya ta jajanta wa Faransa
Haka zalika Yarima William zai tattauna da mai dakin shugaban Amurka mai barin gado Jill Biden gabanin fara taron, kamar yadda masarautar ta sanar.
karin bayani:'Yan sandan Burtaniya sun cafke wanda ya gabza motarsa da kofar fadar masarautar kasar ta Buckingham
Ganawar William da Trump ta karshe ta gudana ne a shekarar 2019, a wata ziyarar aiki da Mr Trump din ya kai Burtaniya lokcin zangon mulkinsa na farko, kuma ziyarar William ta karshe a Paris ita ce wadda ya kai a shekarar 2017 tare da mai dakinsa gimbiya Katr, jim kadan bayan fitar Burtaniya daga kungiyar EU wato Brexit.