Yarjejeniya tsakanin gwamnatin Mali da Abzinawa
June 21, 2013A wannan makon yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin Mali da Abzinawan kasar ta fi daukar hankalin jaridun na Jamus. A labarin da ta buga inda ta bayyana yarjejeniyar da wata alama mai muhimmanci ga Afirka, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a fadin kasar ta Mali sannans sai ta ci gaba kamar haka.
"Makonni biyar gabanin zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a Mali, 'yan tawayen Abzinawa na kungiyar MNLA da gwamnati sun amince da shirin tsagaita wuta. Yarjejeniyar wadda aka sanya wa hannu a ranar Talata a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, ta ba wa sojoji da hukumomi damar shiga garin Kidal mai muhimmanci da kuma yankunan dake kewaye da shi domin samun sukunin gudanar da zabukan a fadin kasar baki daya."
Yarjejeniya a makare
Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci ga yarjejeniyar wadda ta ce an dauki tsawon lokaci kafin bangarori biyu su amince da ita.
"An cimma matsaya a tattaunawar da aka yi tsakanin 'yan tawayen Abzinawa a Kidal dake arewacin Mali da kuma gwamnatin wucin gadin kasar, wannan kuwa zai ba da damar gudanar da zaben shugaban kasa a fadin yankunan kasar ta Mali. Tun a farkon wannan wata na Yuni ya kamata a ce an gama wannan tattaunawa kai tsaye tsakanin gwamnatin birnin Bamako da Abzinawa, amma sabanin ra'ayi musamman game da ikon gwamnati a fadin kasa da girke dakaru ba tare da tsangwama ba da kuma kwance damarar mayakan 'yan tawaye suka kawo cikas. Don hana aukuwar wani tashin hankali a Kidal da kewaye, daga watan Yuli za a girke sojojin ketare da za su aiki karklashin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali."
Gaggawa don gudanar da zabe
Robert Mugabe da masu adawa na takaddama game da ranar gudanar da zabe inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai mayar da hankali ga irin fargabar dake zukatan 'yan Zimbabwe game da sake barkewar wani rikici.
"Bisa ga dukkan alamu shugaba Robert Mugabe mai shekaru 89 na saurin samun tabbacin lokacin zaben, inda yake amfani da ikonsa na ganin an gudanar da zabukan a ranar 31 ga watan Yuli, daura da masu adawa da shi a fagen siyasa, wadanda har yanzu yake cikin wani kawancen gwamnatin hadin kan kasa da ba ta aiki, wadanda kuma yake fatan ganin bayansu nan-take. Mugabe dake kan karagar mulki tun a shekarar 1980, ya sanar da ranar gudanar da zaben ne bayan da a karshen watan Mayu, kotun tsarin mulkin kasar ta yi kira da shirya zaben. Bisa dokokin sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka amince da shi a wata kuri'ar rabar gardama, dole a shirya zabe bayan kammala wa'adin majalisar dokoki. A ranar 29 ga watannan na Yuni wa'adin majalisar ke karewa. A wani taro na musamman da ta yi a Maputo, babban birnin kasar Mozambik, kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen kudancin Afirka ta yi kira ga shugaba Mugabe da ya dage lokacin zaben, tana mai cewa ana bukatar lokaci mai tsawo kafin shirya wani sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe