Yarjejeniyar EU da Tunisiya kan 'yan gudun hijira
June 13, 2023A ziyarar tawagar Tarayyar Turai zuwa Tunusiya, dacta kunshi Firaministar Italiya Giorgia Meloni da Firaministan Nethalandas Mark Rutte da shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta nemi kasar Tuniya ta sake matsa kaimi wajen dakile kwarar bakin hauren da ke shiga nahiyar turai yayin da EU za ta bai wa Tunusiya tallafin kudade masu yawa kamar yadda shugabar Tarayyar Turan Ursula von der Leyen ta baiyana.
"Muna son kafa alaka mai karfi da kasar Tunusiya da zamu jima muna cin moriyar juna da tabbatar da tsaron kasashenmu gami da bunkasar tattalin arziki."
A bisa wannan yarjejeniyar, Tarayyar Turai za ta tallafa wa kasar Tunisia da kudade Euro biliyan daya da kuma karin euro biliyan daya da miliyan dari daya don biyan basuka a kasasfin kudin kasar Tunisia, sai dai za a tattauna wannan batun tare da dukkan kasashen kungiyar ta EU 27 don samun amincewarsu.
Bugu da kari, akwai batun tallafin euro miliyan 100 don tallafawa kasar wajen zamanantar da na'urorin hange nesa da fakon bakin haure, gami da saukaka ayyukan ceton gaggawa
Shugaban kasar Tunisia Kais Saed, wanda kasarsa ke fama da matsalar tattalin arziki, yake kuma fuskantar kalubale daga hukumar IMF ya yi murna da tallafin wanda ya ce ya kamata a dinga bitarsa akai akai.
"Tun farko, mun yi koikari na radin kanmu wajen magance matsalar tattalin arzikinmu da hana kwararar bakin haure zuwa kasarmu, amma abun ya gagaremu. Don haka duk wani tallafin da zai taimaka na magance wadannan matsalolin abun a yi maraba da shi ne.To sai dai hakan baya nufin zamu zama yan sanda ga Tarayyar Turai da za ta dinga keta hurumin bakin haure. Dola ne kamar yadda ake kokarin magance matsalar Tunusiya, su ma sauran kasashen da ke da irin wannan matsalar a mangance musu matsalolinsu tun daga tushe."
Kasar da ke yankin arewacin Afirka, wadda ke fama da matsanancin bashi kuma take kan tattaunawa don neman wani daga asusun bada lamuni na duniya IMF ta kasance mashiga ga bakin haure da masu neman mafaka da ke kokarin tsallaka wa Turai.