Tattaunawa kan fitar hatsi daga Ukraine
March 13, 2023Yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine zuwa kasuwannin duniya a baya ya taimaka wajen rage matsalar karancin abinci da yakin Rasha da Ukraine ya haifar.
Bangaren wakilcin Rasha a Geneva ya tabbatar da cewa tuni tattaunawar ta fara gudana a tsakanin bangarorin biyu, sai dai kuma shugaban hukumar kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffith bai yi karin bayani kan tattaunawar ba ga manema labarai a lokacin da ya isa shalkwatar MDD da ke Geneva.
An dai ga yadda yarjejeniyar ta bayar da damar fitar da hatsi daga Ukraine ta takun Bahar Aswad a bara, inda alkalumma suka nuna an fitar da fiye da tan miliyan 24 na hatsi karkashin yarjejeniyar da MDD ta cimma da kasar Turkiya. A ranar 18 ga watan Maris din nan da muke ciki ne za a sabunta yarjejeniyar kai tsaye, face gwamnatocin Moscow da Kyiv sun ki amincewa.
Ko da yake fadar Kremlin ta yi ikrarin cewa ba a mutunta yarjejeniyar fitar kayan abinci da kuma taki daga Rasha ba. A ziyarar da ya kai birnin Kyiv a makon da ya gabata, sakataren MDD Antonio Guterres ya ce sabunta yarjejeniyar na da matukar mahimmanci.