1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar Maastricht dangane da takardun kudi na Euro

Mohammad Nasiru AwalOctober 30, 2003
https://p.dw.com/p/BwX3

Ko da yake yarjejeniyar ta Maastricht ta share fagen hade manufofin kudi da na tattalin arziki, to amma wai shin yaya aka samu nasarar yin haka ne a wata kungiya mai kunshe da kasashe 16 masu bambamcin manufofin da kuma ci-gaban tattalin arziki? Babban abin da aka fara yi shine an shimfida wasu ka´i´doji ne wadanda dukkan kasashen kungiyar zasu cika a cikin wani kayyadadden lokaci.
Babbar manufa dai a nan ita ce samar da wani kyakkyawan yanayi wanda zai taimaka wajen daidaita karfin tattalin arzikin kasashehn kungiyar. Bugu da kari yarjejeniyar ta Maastricht ta tanadi kafa babban bankin Turai don tabbatar da darajar kudaden musaya tare da kula da farashin kaya da yadda gwamnatoci ke tafiyar da harkokin su na kudi, musamman dangane da daidaita kasafin kudi wato rage cin bashi don kauracewa wani makeken gibin kasafin kudi. Duk kasar da ta kasa cika wadannan sharudda to ba za´a karbe ta a cikin gamayyar takardun kudin na Euro ba. A wancan lokaci Jamus na daya daga cikin kasashen da suka fi kira da a tsananta wadannan sharudda. To amma yanzu Jamus wadda ke fama da matsalolin gibin kasafin kudi ta kasa cika wannan sharadi. Yayin da kasashen kudancin Turai kamar su Spain da Portugal suka samar da nagartattun hanyoyin magance hauhawar farashin kaya da rage gibin da suke samu a kasafin kudinsu bisa al´ada.
A cikin shekarar 1998, ofishin kididdiga na tarayya dake birnin Wiesbaden ya ba da sanarwar da ta ba kowa mamaki, inda a ciki ofishin yayi bayanin cewa a shekarar 1997, Jamus ta ci bashi na kudi DM miliyan dubu 102 wanda yayi daidai da gibin kasafin kudi na kashi 2.7 cikin 100 a wannan shekara, sannan shekara daya bayan haka aka samu gibin kasafin kudi na kashi 3.6 cikin 100.
A cikin watan mayun shekarar 1998, kasashe 11 da suka cika ka´i´dojin yarjejeniyar Maastricht dangane da kirkiro kudin Euro a wannan lokaci, sun gudanar da wani taron koli na musamman a birnin Brussels, don kawad da wani shinge na karshe akan gamayyar takardun kudi na Euro. A ran daya ga watan janerun 1999 kuwa aka shiga zagaye na uku na amfani da kudin Euro, wanda hakan ya ba da damar fara aikin babban bankin Turai dake birnin Frankfurt.
To sai dai yanzu ana iya bayyana hakan da cewa ya zama tarihi, domin duk da cewa har yanzu akwai masu magana game da ka´i´dojin yarjejeniyar ta Maastricht, amma ba´a ba da muhimmancin da ya kamata game da tanadin jan kunne da wannan yarjejeniya ta yiwa kasashen da suka kasa cika ka´i´dojin rage cin basussuka ko gibin kasasfin kudinsu.