Yarjejeniyar tsagaita hari kan fararen hula
October 31, 2020Talla
Bangarorin biyu sun cimma wannan matsayar ce a tattaunawar sulhu da suka gudanar ranar Juma'a a birnin Geneva.
Kasashen biyu sun kuma amince za su yi musayar fursunonin yaki da kuma gawarwakin mutanen da aka kashe a filin daga nan da mako guda a cewar kungiyar kawancen tsaro da raya tattalin arzikin nahiyar Turai OSCE wadda ta jagoranci tattaunawar.
Hakan nan kuma bangarorin biyu za su mika tambayoyi da kuma bayanai a rubuce game da hanyoyin da suke gani sun fi dacewa don cimma tsagaita wuta bisa ka'idojin da aka amince da su a taron da ya gudana a Moscow a ranar 10 ga watan Oktoba.