Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tana aiki
August 27, 2014Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka amince tsakanin Isra'ila da Ƙungiyar Hamas a Zirin Gaza tana aiki. Sojojin Isra'ila sun ce ba su kai wani farmaki ta sama a kan Gaza ba, kana ba a harba rokoki daga Gaza zuwa Isra'ila ba. Da yammacin ranar Talata ɓangarorin biyu suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dogon lokoci bayan sun kwashe makonni bakwai suna yi wa juna ɓarin wuta. Ƙasar Masar ce ta shiga tsakani aka yi sulhun. Dubun dubatan mutane a Zirin Gaza sun kwashe dare suna bukukuwa a kan tituna dangane da yarjejeniyar tsagaita wutar. Aida Najjar daga yankin Khan Yunis cewa ta yi: "godiya ta tabbata ga Allah, mun yi farin ciki da wannan yarjejeniyar. Mun samu sa'ida yanzu. A baya mun kasance cikin yanayi na fargaba."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane