Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
August 27, 2014Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-moon ya ce yana fatan cimma wannan yarjejeniya zai share fagen bin hanyoyin siyasa domin samun dorewar zaman lafiya na din-din-din a yankin. Daga cikin tanade-tanaden yarjejeniyar dai Isra'ila ta amince ta fara bude kan iyakokin yankin na Zirin Gaza domin bada damar shigar da kayan agaji da suka hadar da abinci da magunguna da kuma kayayyakin gine-gine bisa sanya idanun hukumomin Palasdinu a wani mataki da Isra'ilan ta ce ta dauka domin dakile shigar da kayan yaki ga kungiyar Hamas. Dubun dubatar Palasdinawa ne dai suka mamaye kan titunan Zirin Gaza suna murnar samun galaba a yakin na tsahon kwanaki 51 da ya hallaka rayukan Palasdinawa sama da 2,100 wanda kiyasi ya nunar da cewa mata da kanana yara ne suka fi mutuwa, yayin da harin rokokin da kungiyar Hamas ta kai Isra'ilan ya yi sanadiyyar mutuwar Yahudawa 69.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu