Gwamnati da Abzinawa a Mali sun tsagaita wuta.
June 5, 2015Talla
Hakan dai ya bada karfin gwiwa wajen cimma yarjejeniyar sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ta jima ta na kokarin ganin an cimma a tsakaninsu domin kawo karshen yakin da suka kwashe tsahon shekaru suna fafatawa da juna a arewacin kasar. Babban jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Malin Mongi Hamdi ne ya sanar da hakan inda ya ce daya daga cikin matakan yarjejeniyar ya bukaci da a tsagaita wuta a garin Menaka da ke arewaci da kuma janyewar mayakan sa kai da ke goyon bayan gwamnatin ta Mali a yankin, inda ya ce za a maye gurbinsu da dakarun Majalisar Dinkin Duniya zuwa wani lokaci. Su dai 'yan tawayen Malin na fafutukar samar da 'yancin kan yankin Abzinawa ne wanda suka yiwa lakabi da Azawad.