Tsagaita wuta a Yemen
December 17, 2018Talla
Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa a wannan Talata za a fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, domin kawo karshen rikicin da ke faruwa a garin Hodeida da kewaye na kasar Yemen. Haka sakamakon yarjejeniyar da aka kulla a kasar Sweden tsakanin gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya da kuma 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran.
Jami'in na Majalisar Dinkin duniya da ya yi magana da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya bukaci a sakaye sunansa. A karshen mako mazauna garin na Hodeida da ke Yemen sun bayyana gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin inda mutane da dama suka halaka.