1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yarjejeniyar Gaza ta kare ba tare da jin karin bayani ba

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 1, 2023

Isra'ilar dai ta koma fagen daga bayan zargin Hamas da karya yarjejeniyar ta hanyar fara harba mata rokoki

https://p.dw.com/p/4ZeQR
Hoto: Israel Defense Forces/REUTERS

Da safiyar Litinin din nan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta kare, ba tare da jin wani karin bayani daga Qatar da ke shiga tsakani ba, ko kuma Masar da Amurka da ke tallafa mata, lamarin da ke nuna cewa yakin ka iya ci gaba.

Karin bayani:Gaza: Masar da Qatar na neman a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta

Isra'ilar dai ta sanar da komawa fagen daga don ci gaba da yakin, bayan da ta zargi mayakan Hamas da karya yarjejeniyar ta hanyar fara harba mata rokoki, wanda tuni sojojinta suka kakkabo su.

Karin bayani:Dubban mazauna Gaza sun kwashe abincin agaji

Kafin karewar wa'adin dai, kungiyar Hamas da wasu kasashen yamma suka ayyana a matsayin ta ta'addanci, ta sako mutane sama da dari daga cikin 240 da ta yi garkuwa da su, a lokacin da ta kai wa Isra'ila farmaki a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

Rikicin dai ya hallaka Falasdinawa sama da dubu goma sha biyar, yayin da su ma 'yan Isra'ila dubu daya da dari hudu suka halaka.