1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar warware rikicin siyasar Pakistan

January 17, 2013

Masu bore a Pakistan sun cimma yarjejeniyar dakatar da zangan-zangar adawa da gwamnati.

https://p.dw.com/p/17MZs
Pakistan Long March DW/ Shakoor Raheem When was it taken: 15.01.2013, in Islamabad Security arrangements.Main stage for long march in Blue area Islamabad.Participants of the Long aMarch
Hoto: DW/ S. Raheem

Jami'ai a Pakistan sun sanar da cewar gwamnati da kuma wani shaihin malamin da ke jagorantar gangamin nuna adawa da gwamnati na tsawon kwanaki hudu kenan a jere, sun cimma yarjejeniyar da za ta kai ga jinginar da boren, wanda dubbannin 'yan kasar ta Pakistan ke halarta a Islamabad, babban birnin kasar. A dai yammacin wannan Alhamis ne jami'an suka ce gwamnati ta kulla yarjejeniyar tare da Tahir ul-Qadri.

Dama dai shaihin malamin na neman a rusa gwamnatin da ke mulki a Pakistan, tare da maye gurbinta da wata gwamnatin wucin gadi, game da samar da sauye-sauyen siyasar da za su kai ga yin watsi da 'yan siyasar da ke da laifin cin hanci daga harkokin mulki.

Wani mamba da ke halartar taron sulhun ya ce gwamnati ta amince ta rusa majalisar dokokin kasar - kwanaki kalilan gabannin cikar wa'adinta a cikin watan Maris, lamarin da zai bada damar kimanin kwanaki 90 gabannin gudanar da sabbin zabuka. Wani jami'in gwamnati ya ce tuni firayiministan ya sanya hannu akan yarjejeniyar. Sai dai dukkan jami'an da suka sanar da hakan sun bukaci a sakaya sunayensu domin ba a basu umarnin yin tsokaci akan batun ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman