Yau ake gudanar zaben kasa a Yuganda
February 18, 2016Talla
Manyan wadan ke fafatawa a zaben dai su ne shugaba mai ci Yoweri Museveni wanda ke mulkin kasar tun shekaru 30 da suka gabata da kuma kuma babban abokin adawa Kizza Besigye.
Ana dai yi wa zaben na wannan Alhamis kallon wanda aka fi fafatawa mai karfi tun bayan dawowar kasar a tsarin jam'iyyu masu yawa a shekara ta 2005.
A yanzu haka dai birnin Kampla kusan ya yi tsit, bayan da magoyan bayan Besigye suka gamu da fushin 'yan sanda wadanda suka yi ta fesa musu hayaki mai sa kwalla.
Masu lura da al'amuran kasar na cewa shugaba Museveni zai iya yin nasarar zarcewa, to amma akwai alamu idan zaben ya zo kankankan, 'yan adawa na iya gudanar da bore.