1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau za a fara taron kolin Yankin Gabas ta Tsakiya a Amirka

Ibrahim SaniNovember 27, 2007
https://p.dw.com/p/CTZP

A nan gaba kaɗan za a fara taron ƙolin yankin gabas ta tsakiya, a birnin Annapolis ɗin ƙasar Amerika. Rahotanni sun ce wakilan ƙasashe da kuma ƙungiyoyi sama da hamsin ne za su halarci wannan taro, a ƙoƙarin samo bakin zaren warware rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya, musanmamma a tsakanin Israela da yankin Falasɗinawa.Tuni shugaba Bush ya yi maraba da mahalarta taron a fadar White-House, ciki har da Faraministan Israela Ehud Olmert da takwaransa na Falasɗinawa Mahmud Abbas. A wata liyafar cin abinci da shugaban ya shiryawa mahalarta taron, Mr Bush ya jaddada muhimmancin wannan taro, a tsakanin Israela da yankin Falasɗinawa.Wannan taron koli dai a cewar rahotanni na a matsayin irinsa na farko ne, a tsawon shekaru bakwai da su ka gabata.