Yaushe aka girka Kungiyar Tarayya Turai?
March 19, 2012A shekara 1945 kasashen Turai suka fita daga yakin duniya na biyu inda wasu daga cikin kasashen su ka yaki juna kamar misalin Faransa da Jamus.
Bayan yakin ya kare, kasashen suka yi tunanin kirkiro wata kungiyar da za ta tattara su karsashin wata lema, wadda za ta zama riga kafi ga abkuwar yake-yake,ta haka ne ranar 17 ga watan Maris na shekara 1948 kasashen Faransa, Beljiam, Holand, Luxemburg, da Birtaniya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Brussels,inda suka girka kungiyar farko ta taimakon juna bayan yankin duniya na biyu.
Bayan wannan, ne sai Robert Schuman ministan harakokin wajen Faransa na wacen lokaci, ya gabatar da wata shawara wadda ta tanadi gama karfi tsakanin Turai, mussamman Faransa da Jamus, ta fannin tattalin arziki.
Wannan shawara ta Robert Schuman ta haifar da wata kungiya da aka radawa suna da faransanci la Communauté Europenne de Charbon et de l´Acier, wato kungiyar kasashenTurai mai bunkasa albaratun kwal da karafa.
Bayan wannan kungiya da ta shafi tattalin arziki,sai kuma suka kirkiro kungiyar tsaro da suka sa ma suna la Communauté Europenne de Defense( ECD) wadda ta ba Jamus damar sake mallakar makamai bayan haramcin da aka yi mata a karshen yakin duniya.Sannan kungiyar ta ECD ta bullo da wasu dokoki dake matsayin garkuwa ga kasashen Turai wanda a karkashin su idan aka kaima kasa daya yaki daga cikin kasashen da suka rattaba wa yarjejeniyar hannu, tamkar kawaiwa sauran kasashen yaki ne.
Haka dai sannu a hankali su ka yi ta tunani, suna bullo da dokokin bai daya ta fannoni daban-daban, kamar tattalin arziki, tsaro cinikayya, makamashi zirga-zirga da dai sauransu.
Ranar aihuwar kungiyar EU
A takaice za aiya cewar ranar da cikin aihuwar kungiyar taraya turai ya shiga shine daga ranar tara ga watan mayu na shekara 1950 lokacin da Robert Schumman, ya yi jawabin bada shawara da na yi bayani dazu, wadda kuma ta samu goyan baya daga jiga-jigan kasashenTurai kamar su Konrad Adenauer shugaban gwamnatin Jamus ta yamma a wacen lokaci. Kasashen kuma da suka girka tubalin tushe na tarayya Turai sune:Jamus, Faransa, Belijiam, Italie, Luxembourg da Holland wato kasashe shida kenan.
Wannan suna na EU ko kuma Tarayya Turai ya samo asuli tun daga yarjejeniyar birnin Maastricht a shekara 1992,wani birni ne dake kasar Holland, kusa da iyakokin Jamus da Beljiam.Wannan yarjejeniya ta Maastricht da kasashen Turai suka rattaba hannu ta karfafa hadin kan kasashen ta fannin siyasa da diplomatiya, a cen baya hadin kan ya shafi makamashi, tattalin arziki da dai sauransu amma daga Maastricht sai ka bullo da wamni tsari inda kasashe Turai za su dinga magana da murya daya a fagen siyasar duniya, sannan kuma daga nan a ka bada shawara kirkiro da kundin bai daya na Euro, wanda shine a hanlin yanzu mafi yawan kasashen EU ke amfani da shi tun shekara 1999.
Yawan kasashen Kungiyar EU
A halin yanzu Eu ta kunshi kasashe 27 daidai, da farko kamar yadda muka bayana kasashe shida suka girka ta daga baya aka ta yi ta samun karin 'yan takara, a shekara 2004 misali kasashe goma dukan su dake karkashin mulkin tsohuwar tarayya Soviet suka samu nasara shiga EU, sannan kasashen Bulagriya da Roumaniya su shiga a shekara 2007, kasar Croatiya ta samu izinin shiga ranar dya ga watan Juli na sheklara mai kamawa.
Sannan akwai kasashe da dama wanda a yanzu haka suke bukatar ajje takardar takara shiga rukunin kasashen EU, daga cikinsu akwai Sarbiya, wadda ita a watan da ya gabata a ka karbi takardarta, sanna kwai Bosniya, Montenegro da Kosovo, akwai kuma kasar Turkiya wada itama tun 1987 ta nuna shawar shiga amma har yanzu shiru. Kasashen membobin EU za su cigaba da tattanawa domin tantance cencenta, ta ko kuma rashin cencentar wannan kasashe 'yan takara ta zama membobi a cikin EU.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohammed Abubakar