1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawaitar hare-hare na barazana ga zabuka a Sahel

Zulaiha Abubakar MAB
January 10, 2020

A daidai lokacin da shugabannin yankin Sahel ke shirin gudanar da taron koli da takwaransu na Faransa kan matsalar tsaro, hare-haren ta'addanci na ci gaba da kashe fararen hula da soji a Mali da Najeriya da Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/3W0Wq
Symbolbilder Niger Armee
Hoto: picture-alliance/Zumapress/D. White


Wani sabon rahoto da Majalisar Dibkin duniya ta fitar ya bayyana mutuwar akalla fararen hula da jami'an tsaro dubu 4000 a bara, yayin da a shekru ukun da suka wuce aka samu asarar rayuka 770. 'Yan ta'adda na amfani da iyakokin sa kai da rukunin wasu jama'a ke kirkira saboda bukatar kai, da rikicin kabilanci da raunin a bangaren jami'an tsaro  wajen kaddamar da hare-hare, kamar yadda Mohamed Ibn Chambas shugaban ofishin Majalisar Dinkin Dunya reshen yamamcin Afirka da kuma yankin Sahel ya bayyana.


Ya ce: "Yammacin Afirka da yankin Sahel ya girgiza da yawaitar hare-hren ta''addanci a 'yan watannin nan, yayin jawabina a taron tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya gudana ranar 16 ga watan Disambar bara na bayyana yadda hare-haren da faren hula da sojoji suke fuskana daga bangaren 'yan ta'adda ya haifar da shakku a zukantan mutane." 

Mohamed Ibn Chambas
Ibn Chambas ya bayyana takaici game da yadda yawaitar hare-haren a yankin SahelHoto: picture alliance/AA

 Mohamed Ibn chambas ya dora alhakin matsalolin tsaron a kan tabarbarewar tattlain arziki da sauyin yanayi da kuma rikicin makiyaya da manoma. Masana sun bukaci karin hadin kan kasashen ketare don kawo karshen wadannan matsaloli, game da wannan kalubale na tsaro.   Wadanan matsalolin tsaro na afkuwa ne yayin da sojojin kasashen ketare suke jibge don aikin yaki da ta'addanci. A baya-bayan nan dai hare-haren sun fi karkata ne kan jami'an tsaro, al'amarin da ya sanya al'umma a kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali ke sukar zaman da dakarun kasashen ketare suke yi a yankunansu, 

Burkina Faso Wahl in Ouagadougou
Hare-haren ta'addanci za su iya yin tasiri a kan zabe a kasashen yammacin AfirkaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Yanzu haka dai ofishin Majalisar Dinkin Duniya na yammacin Afirka da yankin Sahel na fatan ganin hare-haren ta'addancin ba za su yi tasari a zaben shugabannin kasashen Togo da Burkina Faso da Cote 'd IVoitre da Ghana da kuma Jamhuriyar Nijar da ke tafe ba