Sayen makamai ya karu a duniya
April 24, 2023Talla
A shekarar 2022 kadai, masu bincike yi gano yadda aka yi ta samun karuwar kudaden da ake kasahewa kan ayyukan soji a duniya da kaso 3.7 cikin 100. Wannan alama ce mafi girma na kowane lokaci kuma yana bin shekaru da yawa na ci gaba da kashe kudi.
Taimakon soja ga Ukraine da damuwa game da karuwar barazana daga Rasha, yayi tasiri sosai wajen tilasta wasu kasashe kashe kudade inganta makaman yaki.
Cibiyar da ke sa ido kan makamai da yaki ta kasa da kasa mai zaman kanta a Sweden, ta ce kasahen Amirka da China da Rasha su ne kan wajen kashe kudin makamai a shekarar 2022 kwatankwacin kashi 56 ciki 100 na kudaden da ake kashewa kan makamai da ayyukan soji a sauran kasashen duniya.