Yawancin 'yan gudun hijirar suna bi ta Bahar Rum
July 1, 2015Talla
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR ta ce tun farkon wannan shekara 'yan gudun hijira dubu 137 sun shiga nahiyar Turai ta amfani da kwale-kwale yayin da sama da 1800 suka rasa raukansu a kokarin shiga Turan ta tekun Bahar Rum. Hukumar ta kara da cewa mafi yawan 'yan gudun hijirar da suka shiga Turan ta tekun Bahar Rum sun cancanci samun kariya karkashin dokokin kasa da kasa. Ta ce akasarinsu suna tserewa ne daga yake-yake da sauran rikice-rikice, wasu kuma gwamnatoci ne ke fatattakarsu. Wannan bayani na kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar ta 'yan gudun hijirar ta wallafa a birnin Geneva.