Yaƙi da cin hanci a jam'iyar Paul Biya
June 14, 2011Jam'iyar RDPC kp CPDM da ke kan karagar mulkin Kamaru ta nesanta kanta daga duk taɓargazar cin hanci da karɓar rashawa da ake zargin wasu daga cikin 'yayanta da aikatawa. Wannan yunƙurin fit da kai ya biyo bayan danganta 'yayan jam'iyar ta Paul Biya da zama matattatar masu halin ɓera da wasu ƙungiyoyin da ke yaƙi da cin hanci a ƙasar kamaru suka yi. Kashi 90 daga cikin 100 na waɗanda kotun ƙasar kamaru ta tuhuma da halarta kuɗin haram ko kuma sama da faɗi da dukiyar ƙasa na da danganta kai tsaye da jam'iyar da ke riƙe da madafun iko wato RDPC ko CPDM.
Daga cikin manyan jami'ab ƙasar da ake zargi da cin hancin, har da tsaffin ministoci da suka haɗa da na kuɗi wato Polycarpe Abah Abah, da na sadarwa wato Mounchipou Seidu da kuma na ilimi wato Halima Haman Adama. Baya ga haka ma akwai darektoci da kuma shugabannin kanfanonin gwamanati kusa talatain da ke zaman jiran hukunci a gidajen yari. Sai dai jam'iyar ta ce ba za ta taɓa ƙyale masu halin ɓera daga cikin 'yayanta su shafa mata kashin kaji ba.
To amma ƙungiyoyin ƙasar ta kamaru sun zargi hukumomi da nuna son kai wajen cafke waɗanda ake zargi da ɓarnatar dua uikiyar ƙasa; suna masu cewa mai makon bincika duk waɗanda ake zargi da aikata ba daidai ba, ana karkarta ne kan masu uwa da wabi, saboda suna shawa'ar zawarcin kujerar shugabancin ƙasa ƙarƙashin wannan jam'ia. Sai dai jam'iyar ta RDPC ko CPDM ta ce babu ƙamshin gaskiya a cikin wannan zargi.
jam'iyar da ke riƙe da madafun ikon Kamaru ta ce za ta ci gaba da jan ɗamara domin ganin cewar ta raba 'yayanta da ruf da ciki da dukiyar ƙasa da suka yi ƙaurin suna a kai. Tuni ma dai ta kafa kwamitin yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa, wanda ta dora ma nauyi tona asirin duk wanda ya ke amfani da matsayin da ya ke da shi domin wawushe kuɗin al'uma.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala