Yaƙin Pakistan
March 30, 2007Talla
A ƙalla mutane 60, su ka rasa rayuka a cikin arangama tsakanin ƙabilu da membobin ƙungiyar Alka´ida a kasar Pakistan a tsukin yan kwanaki 3 da su ka wuce.
Gwamnatin Pakistan na ɗaukar wannan faɗa a matsayin wata nasara,da kuma samun goyan baya daga al´ummar ƙasa , wadda ke sadaukar da rayuwa wajen yaƙar yan taliban.
A shekara ta 2003 dakarun gwamnati Pakistan, sun yi ɓarin wuta da mayaƙan wannan yanki na Waziristan , kamin su rattaba hannu a akan yarjejeniyar zaman lahia, wadda kuma ta tanadi bada haɗin kan ƙabilun a wajen yaƙi da yan taliban.