Yemen: Harin kan shugabannin Al-Qaida
November 26, 2017Talla
Mutanen da ake zaton 'yan jihadi ne na cikin wata mota ce bisa hanyarsu ta zuwa yankin Chabwa, lokacin da jirgi maras matuki da ake zaton na Amirka ne ya buda musu wuta tare da hallakasu baki daya. Kasar Amirka kadai ce ke amfani da jirage marasa matuka a kasar ta Yemen, inda take kai hare-hare musamman ma kan 'yan kungiyar ta Al-Qaida a yankin kasashen na Larabawa. Kungiyar da Amirka ke dauka a matsayin mafi hadari daga cikin rassa na kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi. Kungiyar 'yan jihadi ta IS ma dai ta yi amfani da rashin tsaro na kasar ta Yemen inda ta samu shiga. Kawo yanzu rikicin na Yemen ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 8700 tun daga farkonsa a shekara ta 2015.