Shekaru biyar da fara rikicin Yemen
March 25, 2020Wannan yaki na Yemen tuni ya haddasa yunwa kuma masana na ganin cewa babu wani bangare da ke nuna sassauci kan hanyar dakile rikicin. A watan Maris na shekar ta 2015 jiragen saman yakin Saudiyya suka keta sararin samaniyar Yemen domin kai farmaki kan mayakan Houthi, abin da ke zama farkon yakin da ke kara fadada kan manufa a daya daga cikin kasashe mafiya talauci a yankin Gabas ta Tsakiya.
Saudiyya na jagorantar rundunar taron dangi
Adel al-Jubeir jakadan Saudiyya a kasar Amirka wanda daga bisani ya zama ministan harkokin wajen kasar ta Saudiyya, ya sha alwashin cewa za su yi duk abin da ya dace domin kare gwamnatin Yemen. Shi dai al-Jubeir ya magantu ne bayan da mayakan Houthi suka kutsa babban birnin kasar ta Yemen Sanaa, lamarin da ya tilastawa Shugaba Abdrabbuh Mansur Hadi tserewa zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya, inda ya nemi taimakon soja kwana guda gabanin Saudiyya ta kaddamar da farmakin. A daya bangaren Muhammad Al-Buchaiti shugaban mayakan na Houthi ya nuna cewa hakurin 'yan kasar ya zo karshe daga bangaren Kudu zuwa Arewa.
Corona ka iya kassara kasar baki daya
A shekaru biyar da suka wuce yaki ya yi tasiri na kassara kasar. Fiye da mutane 100,000 suka halaka da suka hada da fararen hula kimanin 12,000 a cewar rahoton kula da rikice-rikice. Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana abin da ke faruwa a Yemen da aikin jinkai mafi muni, inda kimanin mutane 85,000 suka mutu sakamakon yunwa mai nasaba da yakin. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce annobar cutar Coronavirus ka iya rusa tsarin kiwon lafiyar kasar baki daya.
Yakin akida ako kare halastacciyar gwamnati?
Sai dai masana na ganin yakin na Yemen zai ci gaba da dagulewa saboda sabanin ra'ayin da aka saba gani tsakanin kasashe masu goyon bayan Saudiyya da na bangaren Iran da mayakan Houthi. Saudiyya ta shiga cikin rikicin domin dawo da gwamnatin Shugaba Abdrabbuh Mansur Hadi kan madafun ikon Yemen da kuma kare muradunta a kasar, amma yanzu yakin ya sauya salo.