Isra'ila: Netanyahu na son komawa mulki
November 1, 2022Da ma dai tun a bara kafin samar da sabon kawancen da ya kafa gwamnati karkashin jagorancin Yair Lapid ya kawo karshen mulkinsa na shekaru 12, Benjamin Netanyahu ya yi hasashen wargajewar kawancen gamin ganbizan da ya ce wadanda suka hadu kansa haduwar 'yan marina ce. Netanyahu ya sha alwashin dawo wa kan kujerarsa, alwashin da kuma ga dukkan alamu ke kokarin tabbata bayan da kuri'ar da aka kada ranar Jumma'a ta nuna cewa tsoho shugaban na Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi zai iya sake darewa kan mukaminsa. Koda akwai yake tarin zarge-zargen cin-hanci da rashawa da ake masa ya kai shi ga gurfana har sau bakwai gaban kuliya, sai dai ya sha musunta su yana siffanta su da bita da kullin siyasa. A nasa bangaren firaminista mai barin gado Yair Lapid wanda ke son yin tazarce, ya yi kira ga 'yan kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri'a ga jam'iyyun kawancensa.
A na dai ci gaba da kada kuri'a a zaben da shi ne karo na biyar da za a yi a Isra'ilan cikin shekaru hudu, ana kuma fargabar cewa za a iya zuwa karo na shida muddin ba a samu wata ba zata a sakamakon zaben bayan da sakamakon farko ke nuna cewa a yanzu haka kawancen Netanyahu ya samu kujeru 60 daga cikin 120 da ake da su a majalisar Isra'ilan ta Kniseet kana kuri'a daya tal ce ta rage masa ya sake kafa gwamnati. To sai dai matakin da tsohon ministan tsaron Isra'ilan Benny Gantz da ke cikin gwamnatin Netanyahu yake shirin dauka, na bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar firaminista da bai wa jam'iyyun masu sassaucin ra'ayi rinjaye a majalisar na neman dagula lissafin Netanyahun duk kuwa da kara samun karbuwa da yake wajen masu tsattsauran ra'ayi bayan da ya sha alwashin hana Larabawan Isra'ila kada kuri'a a zaben da kuma rusa yarjejeniyar rabon iyaka da arzikin man fetur da iskar gas da gwamnatin Lapid ta cimma a makon daya gabata da kasar Lebanon.