1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yoweri Museveni ya yi rantsuwar kama aiki

Mouhamadou Awal BalarabeMay 12, 2016

Wannan shi ne karo na biyar da Yoweri Musveni ke rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Yuganda. Sai dai 'yan adawa suke ce ba shi ya lashe zaben ba.

https://p.dw.com/p/1ImJs
Uganda Präsident Yoweri Museveni in Kampala
Hoto: Reuters/E. Echwalu

Shugaban Yuganda Yoweri Museveni da ya sake lashe zabe a karo na biyar ya yi rantsuwar kama sabon wa'adin mulki, gaban shugabannin Afirka da dama ciki har da Omar Hassan el-Beshir na Sudan wanda kotun ICC ke neman dankewa. Shi dai Musveni mai shekaru 75 da haihuwa wanda ya dare kan kujerar mulkin Yuganda tun shekarar 1986, ya samu kashi 60 daga cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Sai dai 'yan adawa na ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben na shugaban kasa, suna masu zargin shugaba Museveni da amfani da karfin iko wajen neman zarcewa. Tun gabanin rantsuwar ne gwamnati ta Yuganda ta toshe kafofin sadarwa na zamani bisa dalilan da ta dangnata da na tsaro. Sannan kuma jami'an 'yan sanda suka tsare madugun 'yan adawa Kizza Besigye.

Amma kafin ya shiga hannun hukuma Mista Besigye ya sake nanata cewar rantsuwar kama aikin bata kan turba, inda ya ce. "duk wata rantsuwar da Yoweri Musveni zai yi, ba a yi ta kamar yadda kundin tsarin mulki kasar Yuganda ya tanada ba, domin kuwa ba shi ne ya lashe zaben shugaban kasa ba."