Yuganda: An ba da belin 'yan adawa
August 27, 2018Talla
Bobi Wine wanda asalin sunansa shi ne Robert Kyagulanyi, ya bayyana a ranar Litinin hannunsa dauke da sandar taimakawa masu nakasa a kafa. Wine dai ya yi zargin cewa shi tare da wasu abokan aikinsa an gana masu azaba lokacin da ake tsare da su.
Wani dan firsinan an nade hannunsa da bandeji, sannan biyu daga cikin wadanda ake tsare da su lokacin zaman kotu sun zube a kasa. Sai dai Shugaba Yoweri Museveni ya ki amincewa da batun cewa an ci zarafin mutanen da ke zama 'yan adawa da aka tsare kamar yadda suka yi ikirari. Kotun dai da ke arewacin garin Gulu ta ba da belin wadanda take tsare da su ne bisa dalilai na rashin lafiya.