Masunta 33 sun shiga kurkuku a Yuganda
July 28, 2018Talla
Wata kotu a kasar Uganda ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu zuwa uku ga masuntan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango 33, kotun dai ta ce ta sami mutanen da saba ka'idojin yin su tabkunan mafi tasiri a kudancin kasar.
Wani jami'in kula da ayyukan su a Yuganda ya ce wannan hukuncin ba ya nufin cin fuskan ga makociyar kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sai don nuna bukatar bin dokokin kamun kifi.
An dau lokaci ana samun tsamin dangantaka kan rikicin kamun kifi tsakanin mazauna yankunan da ke kan iyakar kasashen biyu, abinda ke haifar da zaman doya da manja tsakanin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Yuganda.