Yuganda ta fito da salon murkushe adawa
September 30, 2019Talla
Gwamnatin kasar ta sauya wa sojoji hularsu ta aiki, inda hukumomin suka mayar da jar hular da matashin dan adawar nan Bobi Wine ke sanyawa a matsayin na dakarun kasar.
Shi dai Bobi Wine ya yi kaurin suna ne wajen sanya wasu tufafinsa na al'ada tare da jar hula ta mangwamare da aka fi sani da baret, tufafin da magoya bayansa da dama ke amfani da su.
A yanzu sanya tufafin da ake ganin na gwagwarmaya ne, na iya zama sanadin daure duk wani da aka samu na amfani da su a Yugandar.
Matashin dan siyasar dai ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara da Shugaba Yoweri Museveni na kasar a zaben 2021, yana kuma da miliyoyin magoya baya, wadanda galibinsu matasa ne.