1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kungiyoyi masu zaman kansu na cikin tasku

Suleiman Babayo
November 18, 2024

Ana kara samun karancin kungiyoyi masu zaman kansu a kasar Yuganda sakamakon tsauraran matakai da gwamnati ke dauka kan kan kungiyoyi masu zaman kansu a kasra da ke yankin gabashin Afirka.

https://p.dw.com/p/4n86T
Masu gwagwarmaya a Yuganda
Masu gwagwarmaya a YugandaHoto: BADRU KATUMBA/AFP/Getty Images

Lauyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Yuganda sun bayyana cewa an samu raguwar rigistan kungiyoyi masu zaman kansu sakamakon tsauraran matakan da gwamnati ta dauka kan kungiyoyin wadda take cewa sun zama 'yan aiken kungiyoyin kasashen duniya. A shekara ta 2021 gwamnatin ta rufe kungiyoyin masu zaman kansu 54 wadanda ta ce sun gaza cika sharudan da aka gindaya. Sannan tun bayan annobar cutar corona virus gwamnati ta karfafa matakan dakile kungiyoyi masu zaman kansu.

Karin Baynai: An yanke wa 'yan adawa 16 hukunci kan yaudara a Yuganda

Shugaba Yoweri Museveni na kasar ta Yuganda ya shafe shekaru 38 yana rike da madafun ikon kasar da ke yankin gabashin Afirka, kuma yana kara daukan matakan dakile 'yancin fadin albarkacin baki.