Matsalolin masu cutar amosanin jini
May 22, 2024Rahotanni sun nunar da cewa, duk wanda cutar amosanin jini ta yi wa kamun gaske yana jariri to da wuya ya shekara biyar a duniya. Wadanda suke fama da cutar na shan tsangwama saboda ana iya haifar yaro da cutar, idan daya daga mahaifansa na da ita. Malaman addini da kuma 'yan uwa na kin daura aure tsakanin wadanda gwajin jininsu, ya nuna alamun yiwuwar haifar yaran da ke dauke da cutar ta amosanin jini ko kuma Sikcle Cell Anemia. Barbara Nabulo na fama da cutar ta amosanin jini, amma duk da haka ta yi aure kuma ta haifi 'ya'ya uku. Danta na farko yana da shekaru bakwai sannan ta haifi tagwayenta mata a shekarar da ta gabata.
Mai shekarunta 37 tana zuwa asibitin yankin Mbale da ke gabashin Yuganda, tare da fafutukar wayar da kan jama'a kan yadda ake rayuwa da cutar amosanin jinin. Guda daga cikin likitocin da ke kula da yara masu dauke da wananan cutar a sibitin Mbale Dakra Julian Abeso ta ce, ana samun ci gaba a fannin kula da masu dauke da wannan cuta. irin wadannan marasa lafiya. Ko da yake wani sabon nau'in magani da aka amince da shi a Amurka a shekarar da ta gabata na nuna alamun akwai nasara sosai, to amma duk da wannan akwai kuma fargaba saboda tsananin tsadarsa.