140909 IAEA Amano
September 15, 2009Ƙasahe 150 membobin hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nukliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya sun zaɓi Yukiya Amano ɗan ƙasar Japan a matsayin saban shugaban hukumar IAEA da zai gaji Mohamed El Baradei.
Yukiya Amano ɗan shekaru 62 a duniya shine shugaban hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nukiliya na tara,Kuma ƙurrare ne ta fannin ilimin nukiliya.Ya kasa abokin hamayarsa, Abdul Samat Minty na ƙasar Afrika ta Kudu a gwagwarmayar neman wannan matsayi.
Amano ya samu cikkakar shaida daga ƙasashen duniya a game da cencentar sa, saidai wanda suka ɗora masa yaunin, sun yi kira da babbar murya zuwa gare shi ,na yayi iya ƙoƙarinsa, domin warware matsalar nukiliyar da ta ƙi ci ta ƙi cenyewa.
Shi kuwa jikadan Iran a cibiyar hukumar IAEA dake birnin Vienna ya bayyanana buƙatar ƙasarsa tare da cewa:
" Ya kamata Amano ya koyi da kyakkyawan halaye na Mohamed Albaradei, mussamman ta hanyar burjenawa umurnin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, dake son cilasta masa ya bayyana rahoton ƙage.Muna kira gare shi yayi takatsantansan."
A wani taƙaittacen jawabin da ya gabatar jim kaɗan bayan da aka zaɓe shi Yukiya Amano yayi yaba irinaikin da magabacinsa Mohamed AlBaradei yayi a hukumar IAEA,sannan alƙawarta aiki wurjanjen don cimma tudun dafawa.Saidai a cikin jawabin nasa bai ambaci sunan Iran ba, wadda a halin yanzu ke kanun labaran duniya game ada rikicin nukiliya.
"Ina fatan hukumar IAEA zata taka rawar gani ta fannin kawo karshen rikicin nukiliyar Korea ta Arewa."
ƙasashe shidda ne a halin yanzu ke tattana rikicin na Korea ta Arewa ba tare da cimma tudun dafawa ba.
Sannan wani babban ƙalubale dake gaban Amano shine rikicin nukilyar ƙasar Iran, duk da cewar shugaban mai barin gado Mohamed El Baradei ya bayyana gamsuwa agame da cigaban da aka fara samu ta fannin gano bakin zaren warware rikicin.
A makon da ya gabata, shugaban ƙasar Iran ya ambata bada haɗin kai , to saidai a wani abu mai kama da tafiyar hawaniya shugaban daga bisani ya jaddada aniyarsa ta bunkassa nukiliya, sannan ya yi shjagube ga Amurika a game da takunkumin karya tattalin arzikin da ta ɗorawa Iran, wanda a cewar Ahmadinedjad bayi tasiri ba. Mahamud Ahmadinedjad .
Ranar 1 ga watan Desember na wannan shekara Yukiya Amano zai kama ragamar mulki,kwanaki kaɗan bayan babban taron da zai haɗa ƙasashen duniya a game da rikicin nukiliyar Iran, da zai haɗa hukumomin Teheran da tawagogin ƙasashe shidda masu ruwa da tsaki a wannan tattanawa.
Mawallafi:Meyer-Feist/ Yahouza
Edita: Awal