Yunƙurin Isra'ila na zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya
May 31, 2012Gwamnatin Isra'ila ta miƙa gawawwakin palesdinawa 91 da ta shafe shekaru ta na riƙe da su ga hukumomin yankinsu a wani mataki da ta kira na yunƙurin jin ƙai. Ofishin firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewar ya yi hakan ne da nufin mutunta sharuɗan da aka gindaya da za su kai ga samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin gabas ta tsakiya. An gudanar da addu'o'i da kuma bikin karrama gawwakin 'yan palesdinun da suka yi fafutukar ƙwato wa yankinsu 'yanci a fadar mulki ta Ramallah, kafin daga bisani a miƙasu ga hannayen iyali da sauran dangi.
Tun a ranar 14 ga wannan wata na mayu ne Netanyahu ya yi alkawarin miƙa gawawwakin 'yan palesdinu da suka rasa rayukansu tun daga lokacin mamaya ta 1967 wato 45 ke nan da suka gabata. Daga cikin waɗannan gawawwakin kuwa, har da na dangin wani sojan ƙundunbala na ƙasar Lebenon. Wannan yunƙurin ya zo ne a daidai lokacin da shugaban Jamus Joachim Gauk ya ke kammala ziyarar aiki na kwanaki huɗu a yankin gabas ta tsakiya da nufin ƙarkafa ɗankon zumunci da kuma gano hanyoyin girka zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi