Yunƙurin Jamus na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya
May 29, 2012Shugaba Joachim Gauk na Jamus ya fara ziyarar aiki da ke zama na farko a yankin gabas ta tsakiya tun bayan ɗarewarsa kan karagar mulkin ƙasarsa. A lokacin da ya isa Isra'ila inda ya gana da shugaban ƙasa Shimon Peres, Gauk ya jadadda aniyar Jamus na kare muradin bani yahudu da kuma ci gaba da ƙarfafa dankon zumunci tsakanin ƙasashen biyu. Hakazalika, shugaban na Jamus ya nuna mahimmacin samar da 'yantaciyyar ƙasar Palesɗinu a yankin gabas ta tsakiya. Game da batun shirin nukuliyar Iran kuwa, Joachim Gauk ya ce babbar barazana ce ga ƙasar Israila da ma dai yankin baki ɗaya.
Shugaba ya ce Jamus za ta ci gaba da amfani da hanyoyin dipolomasiya wajen ganin cewar an warware matsalolin yankin gabas ta tsakiya cikin ruwan sanyi. Joachim Gauk da kuma takwaran aikinsa na IsraIla Shimon Peres sun halarci bikin tunawa da kisan kiyashi da aka yi wa yahudawa, inda suka ajiye furanin da nufin karrama yahudawa miliyon shida da 'yan nazis suka hallaka. Ranar alhamis ne idan Allah ya kaimu shugaba Gauk na Jamus zai isa birnin Ramallah domin ganawa da shugaban palesdinawa Mahmood Abbas.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita:Usman Shehu Usman