Yunƙurin Paul Biya na yin tazarce a Kamaru
January 6, 2011Su dai ƙusoshin jam'iyar da ke riƙe da mulkin kamaru sun dogara ne akan dokokin RDPC ko CPDM wajen neman tsayar da Paul Biya a takarar shugabancin ƙasar. Bisa ga tsarin jam'iyar dai, wanda ke riƙe da shugabancin RDPC ko CPDM ne, ɗan takara na hallak a zaɓen shugaban ƙasa. A saboda haka babban taron tsayar da ɗan takara ba shi da wani mahimmaci a garesu, illa ya kasance na ran sarki ya daɗe.
Sai dai fa rabon jam'iyar ta gudanar da babban taro domin sabonta wa'adin shugabncin Paul Biya ko ma dai sauran waɗanda ke riƙe da manyan mukamai tun shekaru da dama da su gabata. Lamarin da masu lura da al'amuran siyasar ƙasar Kamaru ke dangantawa da wani salo na gudanar da mulkin kama karya ƙarkashin jam'iyar ta RDPC ko CPDM. Kazalika duk ƙusoshin jam'iyar da suka bayyana aniyarsu ta ƙalubalantar shugaba Paul Biya a lokacin babban taron da suka yi ta kira da a gudanar na tsare bisa zargin cin hanci da karɓar rashawa.
Shi dai Paul Biya ya ɗare kan karagar mulkin kamaru ne tun shekaru 29 da suka gabata. Duk da ƙaddamar da mulkin demekaraɗiya da aka yi a ƙasar bayan kaɗawar guguwar demokaraɗiya a farkon shekarun 1990, Biya ya ci gaba da kakkange madafun iko. A baya-bayannan ma ya kwaskware kundin tsarin mulkin ƙasar domin samun damar yin tazarce a zaɓen shugaban kasa da zai gudana a watanni kalilan masu zuwa.
Muna ɗauke da hira da muka yi da Mouhamadou Bassirou Arabo na jam'iyar RDPC ko CPDM.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu